Romans 9

Zaɓen Allah Mai Iko Duka

1Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi-ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki—  2Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. 3Gama da so na ne, sai a laʼanta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ʼyanʼuwana, waɗannan na kabilata, 4mutanen Israʼila. Su ne Allah ya mai da su ʼyaʼyansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawarai. 5Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.

6Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Israʼila ne suke Israʼila na gaske ba. 7Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ʼyaʼyan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” 8Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ʼyaʼyan Allah ba, aʼa, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. 9Ga yadda aka yi alkawarin nan: “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”
Far 18.10, 14


10Ba ma haka kaɗai ba, ʼyaʼyan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa: 12ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira-aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
Far 25.23
13Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
Mal 1.2, 3


14Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15Gama ya ce wa Musa,

“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,
zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
Fit 33.19

16Saboda haka, bai danganta ga shaʼawar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17Gama Nassi ya ce wa Firʼauna: “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
Fit 9.16
18Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.

19Waninku zai iya ce mini: “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20Amma wane ne kai, Ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”
Ish 29.16; Ish 45.9
21Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yǎ gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?

22Haka ma aikin Allah yake. Ya so yǎ nuna fushinsa yǎ kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa-waɗanda aka shirya domin hallaka? 23Haka kuma ya so yǎ sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka—  24har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Alʼummai? 25Kamar yadda ya faɗa a Hosiya:

“Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba;
zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
Hos 2.23

26kuma,

“Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu,
‘Ku ba mutanena ba,’
za a ce da su, ‘ʼyaʼyan Allah mai rai.’ ”
Hos 1.10

27Ishaya ya ɗaga murya game da Israʼila, ya ce:

“Ko da yake yawan Israʼilawa yana kama da yashi a bakin teku,
ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
28Gama Ubangiji zai zartar da
hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”
Ish 10.22, 23

29Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa:

“Da ba don Ubangiji Maɗaukaki
ya bar mana zuriya ba,
da mun zama kamar Sodom,
da mun kuma zama kamar Gomorra.”
Ish 1.9

Rashin Bangaskiyar Israʼila

30Me za mu ce ke nan? Ai, Alʼummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya; 31amma Israʼila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba. 32Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen bin ta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.” 33Kamar yadda yake a rubuce:

“Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe
da kuma dutsen da yake sa su fāɗi
wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
Ish 8.14; Ish 28.16

Copyright information for HauSRK